1 Mayu 2026 - 21:18
Source: ABNA24
Limamin Haramin Sayyada Zainab (AS) A Damascus Ya Yi Shahada

Hujjatul-Islam "Sayyid Farhan Hassan Al-Mansur" memba na majalisar malaman Shi'a na Syria, da tsakar yau, an kaia masa harin ta'addanci a yankin Sayyada Zainab (AS) na Damascus.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sa'a guda da ta gabata, sakamakon fashewar bam a titin Fatimiyya a yankin Zainabiyya na Damascus, limamin haramin tsarki na Sayyada Zainab (AS) Hujjatul-Islam "Sayyid Farhan Hassan Al-Mansur" ya yi shahada.

Kafin wannan, wasu rahotanni sun ba da labarin cewa "Sayyid Farhan Hassan Al-Mansur" ya ji rauni, amma cikakkun labarai sun nuna cewa wannan malamin Shi'a ya yi shahada.

Sayyid Farhan Hassan Al-Mansur, memba ne na majalisar malaman Shi'a na Syria kuma limamin haramin Sayyada Zainab (AS), wanda ya yi shahada saboda harin da aka kai masa.

…………………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha